Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-07 18:42:59    
Jama'a 'yan kabilu daban daban na kasar Sin suna murnar cika shekaru 60 da kafuwar kasarsu

cri

Jihar Tibet mai cin gashin kanta tana kudu maso yammacin kasar Sin. A zamanin gargajiya, 'yan tsirarun iyayen gijin bayi manoma ne suke mallakar kayayyakin aiki, abin da ya yi wa bunkasuwar aikin noma da kiwon dabbobi tarnaki da dabaibayi a jihar. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin kuma, an kyautata zaman rayuwar manoma makiyaya a zahiri. A lokacin cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, jama'ar Tibet sun yi ta wake-wake da raye-raye, domin isar da fatan alheri ga kasarsu.

Jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da ke arewacin kasar Sin ta kasance jiha mai cin gashin kanta ta kananan kabilu ta farko da aka kafa a jamhuriyar jama'ar Sin. A cikin shekaru 60 da suka gabata, an tabbatar da hadin kan al'umma da kwanciyar hankali a jihar. Yanzu haka, yawan dukiyoyin da ake samarwa a rana guda a can jihar ya ninka na shekarar 1949 har sau hudu, har ma saurin bunkasuwar tattalin arzikin jihar ya zo na farko a kasar Sin a shekaru 7 a jere. Tong Muchao, wani dan kabilar Elunchun wanda shekarunsa ya tashi daya da na jamhuriyar jama'ar Sin, ya ce, yanzu a gidansa, da telebijin da firji da injin dauraya da kuma wayar tarho duk akwai su, kuma yana jin dadin zaman rayuwarsa. Kamar yadda ya ce,"A sanadiyyar kulawar da jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar suka sanya mana, mu mafarauta 'yan kabilar Elunchun muna zaman wadata kwatankwacin yadda muke fama da talauci a zamanin da. Ina fatan Allah ya ja zamanina da karin shekaru 60, kuma ina fatan za mu kara jin dadin zaman rayuwa, kuma Allah ya kiyaye jamhuriyar jama'ar Sin."

1 2 3