
Kafofin watsa labaran Nijeriya suna ganin cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar ta samar da guraban ayyukan yi ga 'yan gwagwarmayan da suka ajiye makamansu tun da wuri, in ba haka ba, akwai yiwuwar su sake komawa hanyar aikata munanan laifuffuka. Amma samar da guraban ayyukan yi ba wani abu ne mai sauki ba, haka kuma akasarin 'yan gwagwarmayar ba su da cikakken ilimi, shi ya sa suka gaza wajen samun aiki. Manazarta suna ganin cewa, an fara samun sakamako mai kyau wajen bada tayin ahuwa ga masu fafutuka a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur, amma ana bukatar kara yin kokari domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki.(Murtala) 1 2 3
|