Ranar 4 ga wata, rana ce ta cikar wa'adin tayin afuwar da gwamnatin Nijeriya ta yiwa masu fafutuka a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur. Sa'o'i kafin cikar wa'adin, shugabannin 'yan gwagwarmayan yankin da kungiyoyinsu sun bada kai ga gwamnati ta hanyar ajiye makamansu. Manazarta suna ganin cewa, sakamakon tayin afuwar da gwamnatin kasar ta yi, yanayin tsaro a yankin Neja Delta zai samu kyautatuwa, amma ana fuskantar wahalhalu a kokarin shimfida zaman lafiya mai dorewa.
Ranar 25 ga watan Yunin bana, shugaban Nijeriya Alhaji Umaru Musa Yar'Adua yayi tayin afuwa ga 'yan gwagwarmayan yankin Neja Delta, da nuna bukatar su amince da tayin afuwar ta hanyar ajiye makamai kafin ranar 4 ga watan Oktoba. Manyan shugabannin 'yan gwagwarmayan yankin hudu, wato Victor Ben, da Ateke Tom, da Farah Dagogo, gami da Tompolo sun ajiye makamansu kwanakin baya, domin amincewa da tayin afuwar gwamnatin kasar.
Ministan tsaro na Nijeriya, kana shugaban kwamitin kula da tayin afuwa Godwin Abbe ya bayyana cewa, an samu damar cimma dimbin nasarori wajen bada tayin afuwa ga masu fafutuka a yankin Neja Delta. Ya kuma kara da cewa, man fetur ba zai ci gaba da zama ummul aba'isin haifar da rikici ba a wannan yanki, amma zai zama dukiya da samar da zaman alheri ga jama'ar yankin. A waje guda kuma, Mista Abbe ya ce, gwamnatin Nijeriya zata yi hadin-gwiwa tare da dukkanin shugabannin kungiyoyin 'yan gwagwarmaya, ya kuma bada tabbacin cewa, 'yan gwagwarmayan da suka amince da tayin ahuwa ba zasu yi nadama ba.
1 2 3
|