
Amma babbar kungiyar masu fafutukar kwato 'yancin yankin Neja Delta mai arzikin man fetur MEND ta ki amincewa da tayin ahuwar, hakan na nufin cewa har yanzu dai kura ba ta lafa ba a yankin. Kungiyar MEND tana ganin cewa, tayin ahuwa ba zai kai ga warware rikicin yankin Neja Delta ba daga tushe, shi ya sa kungiyar zata ci gaba da yin gwagwarmaya, amma ba zata yi fito-na-fito ba a tsakaninta da dakarun gwamnati, zata yi yakin sari-ka-noke. Dadin dadawa kuma, kungiyar ta MEND ta bukaci gwamnatin Nijeriyar da ta yi shawarwari tare da ita ba tare da bata lokaci ba.
Baya ga babbar kungiyar ta MEND wadda har yanzu dai take fafatawa, gwamnatin Nijeriya tana fuskantar sauran wasu kalubalolin. Abun dake gaba da kome shi ne, yadda za'a yi a tsugunar da 'yan gwagwarmayar da suka amince da tayin ahuwa. Kawo yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta fitar da adadin 'yan gwagwarmayar da suka amince da tayin ahuwa ba, amma an yi hasashen cewa, wannan adadi zai kai dubu 10. Kazalika kuma, domin tabbatar da aiwatar da tayin ahuwa tare da samun nasara, gwamnatin kasar ta ware dala kusan miliyan 64, ciki kuwa har da baiwa kowane dan gwagwarmaya kudin rangwame na Naira dubu 65, amma bayar da kudin rangwame ya gagara kyautata zaman rayuwar 'yan gwagwarmayan cikin tsawon lokaci.
1 2 3
|