
Dadin dadawa kuma, a cikin jawabinsa, shugaba Hu ya sanar da wasu matakai da fatan dai kara taimakawa kasashe masu tasowa, kamar ci gaba da aiwatar da matakan ba da taimako daban daban da aka tabbatar da su a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.
Haka zalika kuma, shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya yi jawabi da cewa, tilas ne kasashen duniya su yi watsi da rikici da sabanin da suka sha fuskanta, kuma bisa tushen samun moriyar juna da girmama juna, su taimakawa juna da hada kai domin warware mabambantan batutuwan da suke fuskanta.
A ranar farko ta wannan babbar muhawara, sauran shugabannin kasashen duniya fiye da 20 su ma sun yi jawabi, inda yawancinsu suka yi kiran inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.(Tasallah) 1 2 3
|