Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-24 17:20:56    
Hu Jintao ya yi muhimmin jawabi a yayin babbar muhawara ta babban taron M.D.D. a karo na 64

cri

Ban da wannan kuma, a cikin jawabinsa, Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kansu, su farfado da ruhun gudanar da harkoki a tsakanin mabambantan bangarori, cikin hadin gwiwa su daidaita kalubaloli daban daban da suke fuskanta.

Mr. Hu Jintao shi ne shugaban kasar Sin na farko da ya yi jawabi a yayin babbar muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya a cikin shekaru 30 ko fiye da suka wuce. A cikin jawabinsa, shugaba Hu ya nuna cewa, a halin yanzu, ya kamata kasashen duniya su gama kansu, su nuna ruhun samun zaman lafiya da bunkasuwa da yin hadin gwiwa da samun nasara tare da kuma yin hakuri, kuma su sa kaimi kan raya duniya mai jituwa da dauwamammen zaman lafiya da kuma wadata tare. Game da wannan, ya yi nuni da cewa, dole ne a kara yin hangen nesa a harkokin tsaron kai da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Wajibi ne a daidaita harkokin bunkasuwa ta wasu fannoni tare kuma da sa kaimi kan samun wadata tare. Tilas ne a kara nuna budaddiyar zuciya a fannin yin hadin gwiwa tare kuma da sa kaimi kan tabbatar da samun moriyar juna da nasara tare. Hazalika kuma, dole ne a kara yin hakuri da nuna wa juna tausayi da zummar yin zaman tare cikin jituwa.

Sa'an nan kuma, shugaba Hu ya jaddada cewa, bunkasuwar kasar Sin tana ba da gudummawa ga kasashen duniya gaba daya tare da samar musu babbar dama. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan bin manufar samun bunkasuwa cikin lumana, da bude kofarta ga waje da nufin cin moriyar juna da samun nasara tare, da kuma yin hadin gwiwar abokantaka da dukkan kasashen duniya bisa ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana.

1 2 3