Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-23 18:14:20    
Ba'a cimma tudun-dafawa ba a yayin shawarwarin Palesdinu da Isra'ila gami da Amurka

cri

A waje guda kuma, manazarta suna ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, yanayin siyasar bangarorin Palesdinu da Isra'ila yana jawo cikas ga yunkurin cimma matsaya a tsakaninsu kan wasu manyan bambance-bambance. A nasa bangare, duk wani sassauci da Benjamin Netanyahu yayi zai fuskanci kakkausar adawa daga kawancen masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila. A ranar 21 ga wata, a birnin New York, Netanyahu ya yi shawarwari tare da ministan tsaron gida na Isra'ila Ehud Barak, da ministan harkokin wajen kasar Avigdor Lieberman har zuwa sanyin safiyar ranar 22 ga wata, inda suka yanke shawarar cewa, a halin yanzu Isra'ilar ba zata yi sassauci ba a kan batun fadada matsugunan Yahudawa a yankin gabashin birnin Kudus. A nata bangare kuma, rikicin da ake yi tsakanin manyan kungiyoyi biyu a Palesdinu wato Fatah da Hamas yana jawo tsaiko ga kokarin da Mahmoud Abbas ke yi na farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinun da Isra'ilar.

Manazarta suna ganin cewa, ko da yake gwamnatin Obama tana kokarin gudanar da shawarwari a tsakanin Palesdinu da Isra'ila da Amurka, haka kuma Obaman ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su yi kokarin nuna sassauci domin cimma matsaya a yayin shawarwarin, amma akwai wasu manyan bambance-bambance da yawan sabani a tsakanin bangarorin biyu, wadanda ba za'a iya warware su ba cikin sauki. Lallai akwai sauran jan aiki a gaba wajen shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila.(Murtala)


1 2 3