Manazarta suna ganin cewa, ko da yake an yi shawarwari tsakanin bangarorin uku, amma akwai bambanci sosai a tsakanin Palesdinu da Isra'ila a kan wasu muhimman batutuwa, kuma bangarorin biyu ba su yi sassauci ba, shi ya sa da wuya ainun a cimma daidaito a tsakaninsu. Hukumar Palesdinawa tana yin tsayin daka kan cewa, ba zata yi shawarwari tare da Isra'ila ba, sai Isra'ilar ta daina ayyukan fadada matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan da gabashin birnin Kudus. Amma a nata bangare, kasar ta Isra'ila ta kawar da kai ga matsin lambar da Amurka ke yi mata, ta amince da a daina wasu ayyukan gina matsugunan Yahudawa tare da gindaya sharadi.
1 2 3
|