
"yan kallo na kasar Nigeriya su ma sun bayar da ra'ayoyinsu a kan sinimar. Wani dan kallo na kasar ya kuma bayyana cewa, da ya ji cewar wai sunan madugun rukunin masu hannu da laifufuka a cikin sinimar shi ne Obasanjo, sai ya barke da dariya, amma da ya yi tunani sosai, sai bai ji dadi ba, ya bayyana cewa, da aka kira wani mai laifi da cewar wai Obasanjo, ainihin abun nan shi ne domin yin adawa da kasar Nigeriya , a gaskiya dai, mutanen kasar Afrika ta Kudu su ma ba su jin dadi sosai.
A internet na "Facebook", wadanda suke yin amfani da internet su ma suke soma kai kararsu ga sinimar din. Yanzu da akwai mutane fiye da 80 da ke cikinsu sun shiga tattaunawa, kuma sun rubuta ra'ayoyinsu fiye da 150. wasu sun ce, wannan ne wata sinima kawai, amma wasu suna ganin cewa, mai tsara sinimar ya bayyana mutanen Nigeriya tamkar yadda wadanda ba su samu wayewar kai ba. Bai kamata ba a bayyana wata kabilar da ba a fahimce ta sosai ba.
A gaskiya dai wannan ba karo na farkon da kamfanin Soni ya sa gwamnatin Nigeriya ta yi fushi ba. (Halima) 1 2 3
|