Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-21 21:12:59    
An hana nuna Sinima mai suna "District Nine" ta kasar Amurka sakamakon sharrin da ta yi wa kasar Nigeriya

cri

A ranar 19 ga wannan wata, gwamnatin kasar Nigeriya ta ba da umurnin hana nuna sinimar dabon kimiyya mai suna "District Nine" ta kasar Amurka a gidajen nuna sinima daban daban na kasar Nigeriya sakamakon sharrin da ta yi wa kasar Nigeriya a cikin wasu wasannin da aka yi a cikin sinimar, a sa'I daya kuma gwamnatin kasar Nigeriya ta nemi kamfanin nuna wasanni na Soni da ya neman gafara daga kasar Nigeriya.

A cikin sinimar, an nuna cewa, kafin shekaru 28 da suka wuce, karo na farko ne wadanda suke zama a wuraren da ke waje da duniya sun sauko duniya, mutanen duniya ba su san wane irin abun da za su kawo wa duniya, saboda haka an yi amfani da wata unguwar da matalauta suke zama a cunkushe na Afrika ta Kudu don gefentar da su, sa'anan kuma an yi wa unguwar suna "District Nine", wato yanki mai lamba 9 ke nan. Ko da ya ke aka sami labarin sinimar a kasar Afrika ta Kudu, amma labarin na da nasaba da makaurata Nigeriya da ke a kasar Afrika ta Kudu, kuma yawancinsu sun zama wadanda suke da hannun haddasa laifufuka, wani madugun rukunin masu hannun da laifufuka da ke cikin sinimar mai suna "Obasanjo" ya yi hakilon banza na yanke hannun na wani babban dan wasan sinimar da kuma hadiye hannunsa don samun karfin da yake da shi, amma sunan tsohon shugaban kasar Nigeriya shi ne "Obasanjo", wani labari daban da ke cikin sinimar ya bayyana cewa, karuwan kasar Nigeriya sun yi kwadayinsu na samun damar haduwa da wadanda suke zama a wuraren da ke waje da duniya.

1 2 3