
Game da wannan, ministar sadarwa ta kasar Nigeriya Dora Akunyili ta bayyana cewa, sinimar "District Nine" ta bayyana cewa, mutanen kasar Nigeriya sun riga sun zama masu hannun da laifufuka da karuwai ko rukunin wadanda ke cinye naman mutane, wannan ya sa mutanenmu su yi fushi sosai da sosai, kuma sinimar ta yi sharri sosai ga mutanen kasar Nigeriya, abin da ba za mu iya yin hakuri da shi shi ne, a cikin sinimar, madugun rukunin masu hannun da laifufuka sunansa shi ne "Obasanjo", danyen aikin din da aka yi shi ne aikin yin adawa da mutanen Nigeriya.
Akunyili ta bayyana cewa, ta riga ta ba da umurni ga hukumar sa ido ga sinima ta kasar don dakatar da nuna sinimar a duk gidajen nuna sinima na kasar nan da nan. Sa'anan kuma, ita kadai ta rubuta wasika zuwa ga kamfanin Soni, inda ta nemi kamfanin ya nemi gafara sakamakon sinimar, yanzu kamfanin bai amsa karar da gwamnatin kasar Nigeriya ta yi ba.
Bayan da aka bayar da umurnin, wani gidan nuna sinima mafi girma da ke birnin Lagos mai suna Silverbird ya riga ya dakatar da nuna sinimar.
1 2 3
|