
Kana kuma a karshen jawabin da Treki ya yi, ya bayyana cewa, zai yi kokarin tuntubar sakatare janar na M.D.D Ban ki-moon domin gudanar da ayyuka kuma zai hada kai da yin shawarwari da kwamitin sulhu na M.D.D daga dukkan fannoni, don tabbatar da samun daidaituwar matsalar.
Bayan da aka bude bikin kaddamar da taron, za a fara muhawara ta shekara-shekara a ranar 23 ga wata, kuma za a shafe mako guda ana yinta, kuma za a kammala babbar muhawara a ranar 30 ga wata, inda shugabanni na kasashe sama da 140 za su bayyana ra'ayoyinsu kan halin da ake ciki tsakanin kasashen duniya da amfanin M.D.D da dai sauran manyan batutuwan duniya. Bisa labarin da aka samu, an ce, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao zai yi jawabi a gun muhawara ta babban taron M.D.D don bayyana ra'ayin kasar Sin kan halin da ake ciki a duniya da kuma manyan batutuwan duniya.(Bako) 1 2 3
|