Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-16 14:40:08    
An kaddamar da babban taro a karo na 64 na M.D.D

cri

A ranar 15 ga wata agogon New York, an kaddamar da babban taro a karo na 64 na M.D.D a birnin New York, hedkwatar M.D.D, yayin da sabon shugaban babban taron M.D.D kuma sakatare mai kula da harkokin kungiyar tarayyar Afrika na kasar Libya Ali Treki ke yin jawabin fatan alheri, ya bayyana cewa, dole ne a yi gyare-gyare ga babban taron M.D.D, don ba da tabbaci ga amfaninsa.

Bayan da Treki ya zama shugaban babban taron M.D.D a watan Yuli na bana, ya bayyana cewa, babban taron M.D.D na wannan karo zai dora muhimmanci sosai kan aikin yin gyare-gyare ga M.D.D daga dukkan fannoni, musamman ma a kan ayyukan yin gyare-gyare ga kwamitin sulhu na M.D.D da farfado da amfaninsa. Kana, a gun taron, za a yi kokari wajen sassaucin mummunan tasirin da rikicin kudi na duniya ke kawowa kasashe masu tasowa, musamman ga shirin raya kasashen Afrika da aka tsara a shekara ta 2000, da tabbatar da shirin samun bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci. Kana, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai da kokarta tare don cimma wannan buri.

1 2 3