Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-16 14:40:08    
An kaddamar da babban taro a karo na 64 na M.D.D

cri

Haka kuma a wannan rana, yayin da Treki ke yin jawabi a gun bikin kaddamar da taro a karo na 64 na M.D.D, ya sake bayyana wannan niyya, ya jaddada amfanin M.D.D, na ba wanda zai iya maye gurbinsa wajen warware matsalolin duniya. Ya ce, shawarwari da samun fahimtar juna manyan hanyoyi ne da za yi amfani da su wajen warware matsalolin duniya. Ba za a iya cimma matsaya guda ba ta hanyar saka takunkumi ko kauracewa, sai kawai hakan zai kara rashin jin dadi da takaici tsakanin kasashen duniya, kana, zai kawo babban lahani ga babbar niyyar kasashen duniya. A halin da ake ciki yanzu, duniya na fuskantar matsalar bambamcin arziki tsakanin mai kudi da matsiyaci da aikin yaki da ta'addanci da rikici da matsalar yunwa da cututtuka, a sakamakon haka, dole ne kasashen duniya su hada kai tare, da warware matsaloli ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa. Mutanen da ke da bambancin launin fata da bambancin addini da bambancin kabilu za su iya samun hadin gwiwa da shawarwari ta M.D.D.

A sa'i daya kuma, ya yi nuni da cewa, M.D.D na bukatar gyare-gyare da samun demokuradiyya, kana babban taron M.D.D da ke wakiltar kasashen duniya shi ma ya samu cikas ne a kan hanyar samun bunkasuwa, kuma ba za a iya gudanar da dukkan kuduran da aka tsaida ba. Sabo da haka, dole ne a yi gyare-gyare ga babban taron M.D.D, domin tabbatar da amfaninsa.

A matsayinsa na wani jami'i daga kasashen Larabawa, Treki ya yi jawabi musamman a kan batun yankin Gabas ta tsakiya, ya ce, an dage warware matsalar yankin Gabas ta tsakiya da tsawon shekaru 60, wannan ya kasance tamkar wata barazana ga kasashen duniya, yana ganin cewa, M.D.D na taka muhimmiyar rawa wajen warware batun Gabas ta tsakiya, dole ne dukkan kuduran da M.D.D ta tsaya za su iya samun gudanarwa.

1 2 3