Bisa wadannan fasahohin da aka samu, aikin daukar mutane da kumbo na kasar Sin ya samu bunkasuwa cikin saurin gaske. A watan Oktoba na shekarar 2003, an harba kumbo mai dauke da mutane na farko, wanda ya dauki Yang Liwei, wani dan sama jannati, zuwa sararin samaniya, inda ya yi yawo har tsawon awoyi 21 da wani abu. Sa'an nan a shekarar 2005, kasar Sin ta sake aiwatar da zirga-zirgar kumbo, inda 'yan sama jannati 2 suka dade a can sararin samaniya har tsawon kwanaki 5. Bayan haka kuma, sai a zuwa watan Satumba na shekarar 2008, lokacin da 'yan sama jannati 3 suka kasance a cikin kumbon Shenzhou na 7 har tsawon kwanaki 3. Sa'an nan, Zhai Zhigang, daya daga cikin 'yan sama jannatin 3, ya yi tafiya a sararin samaniya, irinta na farko a tarihin kasar Sin.
A sa'I daya kuma, Sinawa sun zura ido kan duniyar wata mai nisa sosai. A watan Oktoba na shekarar 2007, kasar Sin ta harba wani kumbo mai binciken duniyar wata, wanda ya kammala ayyukan bincike cikin shekarar da ta biyo baya. Sun Jiadong, darekta mai kula da aikin binciken duniyar wata na kasar Sin, ya ce,
"Kafin hakan, ayyukanmu na sararin samaniya dukkansu a wurarren da ke kusa da duniyarmu ne aka aiwatar da su, inda tazara zuwa duniya ta kai kilomita dubu gomai. Sa'an nan bayan da muka kara samun wasu fasahohi, dole ne mu kai kumbunanmu zuwa sararin samaniya mai nisa, shi ya sa duniyar wata ta zama matakin farko."
Ban da wannan kuma, aikin binciken babban jirgin sama da aka daina yinsa har tsawon shekaru da yawa, ya sake samun goyon baya daga gwamnatin kasar Sin a shekarar 2007, inda aka mayar da shi cikin ajandar aikinta. Kamar dai yadda Gan Liwei, wani shehun injiniya na kamfanin raya fasahar zirga-zirgar jiragen sama na kasar Sin, ya sa ran cewa, kasar Sin za ta samu babban jirgin sama na kanta a shekarar 2020.
"Idan za mu iya samar da babban jirgin sama a shekarar 2020, to, ma iya cewa karfin kasarmu zai karu ainun, haka kuma, fasahar za ta ba da taimako wajen raya sauran sana'o'i."
Za a iya ganin cewa, kasar Sin na kara ba da tasiri a duniya a fannin zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna, ga misalin sabbin jiragen sama na ARJ21 kirar kasar Sin, an sayar da su zuwa Turai da kasashen da ke nahiyar Amurka. Sa'an nan, kumbo mai binciken albarkatun kasa da kasar Sin da kasar Brazil suka samar da shi tare yana amfanawa kasashe da dama. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta harba wasu kumbunan sadarwa a madadin wasu kasashe. (Bello Wang) 1 2 3
|