Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-10 17:40:30    
Saurin bunkasuwar da kasar Sin ta samu kan harkar zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna

cri

Sa'an nan, a kafuwar sabuwar kasar Sin ke da wuya, gwamnatin kasar ta dora muhimmanci kan raya kimiyya da fasaha, haka kuma ta tsara matakan da za a dauka a nan gaba. Zuwa shekarar 1964, wani hayaki mai siffar laima da ya tashi a arewa maso yammacin kasar Sin ya baiwa duniya mamaki, inda kasar Sin ta yi gwajin fasa bom din atam dinta cikin nasara. Sa'an nan bayan shekaru 3 bayan lamarin, kasar Sin ta fashe h-bom nata cikin nasara. Bayan wannnan kuma, a shekarar 1970, kasar Sin ta harba kumbonta na farko zuwa sararin samaniya. Aikin samar da wadannan boma-bomai 2 da kumbo 1 ya kara karfin kasar Sin ta fuskar kimiyya da fasaha, da kuma aikin tsaron kasa, haka kuma ya sa kasar Sin ta samu wani muhimmin matsayi a dandalin kasa da kasa. Har ila yau kuma, ya sa kasar Sin ta samu isassun fasahohi da masanan kimiyya don raya aikin zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna, kamar dai yadda Mei Yonghong, wani jami'in ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, ya yi bayanin cewa,

'A lokacin, kasarmu ta riga ta raya kimiyya da fasaha sosai, ta yadda muka samu ilimin da ya shafi dukkan fannonin da ake bincike a kai, wanda kasashe kadan ne suke da shi. Ban da wannan kuma, mun samu masanan kimiyya da yawa. Abubuwan ne sun sa kasar Sin ta shiga jerin kasashen da ke kan gaba.'

Sa'an nan, zuwa shekarar 1978, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. A daidai waccan lokaci, kasar Sin ta samar da manufar 'mayar da kimiyya da fasaha kan matsayin abubuwa mafi muhimmanci da za su kawo wa kasar albarka', sa'an nan gwamnatin kasar ta sa an aiwatar da wasu ayyukan binciken fasahohi. Ta hakan, cikin shekaru 30 da suka wuce, halin da kasar Sin take ciki ta fuskar kimiyya da fasaha ya canza sosai, inda karfinta yake ta karuwa cikin sauri. Abun da ya sa Sinawa suke jin dadin babban ci gaban zaman rayuwarsu da aka samu bisa bunkasuwar kasar a fannonin kimiyya da fasaha, haka kuma ya sa su alfahari. Sa'an nan alfaharin nan ya kai matsayin koli a lokacin da aka ambaci aikin daukan mutane da kumbo, kamar yadda Madam Wang take cewa,

'Na yi alfahari sosai, domin na ga abun na da alamar cewa, kasarmu ta samu ci gaba sosai kan kimiyya da fasaha, haka kuma karfinta na karuwa. Sa'an nan ina so in fada wa 'yan sama jannatin kasarmu cewa, ku jarumai ne na al'ummarmu!'

An kaddamar da aikin binciken fasahar daukan mutane zuwa sararin samaniya da kumbo a farkon shekarun 1990, sa'an nan an samu fasahohi da yawa ne kafin aka kaddamar da aikin, bisa kokarin binciken fasaha da aka yi cikin shekaru da yawa. Kafin ta harba kumbo mai dauke da 'yan sama jannati, kasar Sin ta riga ta harba kumbunanta iri 15 wadanda yawansu ya wuce 50. Har wa yau kuma, kasar Sin ta samar da rokokin nau'o'I goma da wani abu, wandanda suka kai kumbuna fiye da 70 na kasar Sin da na kasashen waje zuwa sararin samaniya.

1 2 3