Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-10 17:10:18    
Za a kai matsayin da ba a taba gani ba ta fuskar bikin yin fareti da za a yi a ranar bikin kasar Sin

cri


Kungiyoyi masu tafiya da kafa dake yin horo a arewacin karkarar birnin Beijing su ma suna da halin musamman. Mataimakin mai ba da jagoranci na kungiyoyin Guo Zhigang ya gabatar da cewa, Ko da yake yawan sojojin dake cikin kungiyoyi masu tafiya da kafa ya ragu bisa na bikin kasa na cika shekaru 50, amma an kara ire-iren sojoji, ciki kuwa sojojin musamman za su yi bayyanarsu ta farko a yayin bikin.'

Ban da wannan kuma, kungiyoyin sojojin sama za su tuka jiragen sama a lokacin bikin yin fareti. Mataimakin shugaban ofishin furofaganda na sashen siyasa na mayaka na sama Xu Huidong ya bayyana cewa, kungiyoyin sojojin sama da za su halarci biki sun nuna halin musamman a fannoni guda biyar,

'Da farko, yawan ire-iren sojoji, da na sojoji, da kuma na jiragen sama duk ya wuce bisa na bukukuwan yin fareti na da. Na biyu, kayayyakin soja, da sojoji dukkansu su sababbi ne. Na uku, sojojin da za su halarci bikin fitattun sojoji ne masu shiga yaki. Na hudu, wasu kungiyoyi daga cikinsu na hade da jiragen sama na iri daban daban, don haka, da wuya a horar da su tare. Na biyar, ana horar da wadannan sojoji yadda ya kamata.'

Yanzu, akwai sauran kwanaki fiye da 20 kafin bikin kasa, kungiyoyi daban daban da za su halarci bikin yin fareti suna samun horo kamar yadda ya kamata. An yi imani cewa, a ranar 1 ga watan Oktoba, wadannan kungiyoyin soja za su nuna gwanintarsu, don bayyanawa duniya halin musamman na sojojin kasar Sin a zamanin yau.
1 2 3