A zamanin da muke ciki, dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen duniya na kara inganta, kuma makomarta tana da alaka sosai da makomar duk duniya. Yanzu kasar Sin na kara taka rawa a duk duniya, musamman ma bayan abkuwar rikicin kudi a duk duniya, ba ma kawai Sin tana daukar kwararan mataki domin farfado da tattalin arzikinta ba, har ma tana kokarin hada kai tare da kasashen duniya domin shawo kan wannan matsala, haka kuma kasa da kasa sun mayar da hankali da nuna babba yabo ga muhimman shawarwari da gwamnatin kasar Sin ta fitar. Mista Yang ya ci gaba da cewa: "Kokarin da kasar Sin ke yi na hada kai tare da kasashen duniya domin shawo kan matsalar kudi yana bayar da kwarin-gwiwa ga kasa da kasa, lalle tana bayar da muhimmiyar rawa a fannin farfado da tattalin arzikin duniya."(Murtala) 1 2 3
|