Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-10 17:04:36    
Kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa nan da shekaru 60 da suka gabata

cri

Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 60 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, kana shekara ce ta cika shekaru 60 da fara gudanar da harkokin diflomasiyya. Ministan harkokin waje na kasar Sin Mista Yang Jiechi ya ce, a cikin shekaru 60 da suka gabata ne, kasar Sin ta karfafa hadin-gwiwa tare da kasashe daban-daban, da bayar da muhimmiyar gudummawa ta fuskar shimfida zaman lafiya, da neman bunkasuwa a duniya. A halin yanzu, kasar Sin na kara taka rawar a-zo-a-gani a harkokin kasa da kasa.

Yayin da yake hira da wakilin gidan rediyon CRI, Mista Yang Jiechi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin Sin da manyan kasashe daban-daban ta samu bunkasuwa ba tare da kakkautawa ba, alal misali, an kafa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Rasha, haka kuma huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta bunkasa yadda ya kamata. A waje guda kuma, kasar Sin ta nuna hazaka sosai wajen halartar shawarwarin da aka yi tsakanin kasashe hudu na BRIC, da na kasashe biyar dake tasowa, hadin-gwiwar Sin da kasashe maso tasowa na kara samun ingantuwa.

Gudanar da harkokin diflomasiyya tare da kasashe makwabta, abu ne mafi muhimmanci a cikin harkokin diflomasiyya da Sin ke gudanarwar. Mista Yang ya bayyana cewa: "Kasar Sin tana cikin nahiyar Asiya ne, kuma har kullum tana mayar da aikin raya dangantaka tare da kasashe makwabtanta a gaba da kome. A shekarun 1950 na karnin da ya gabata ne, kasashen Sin da Burma gami da Indiya suka fitar da 'muhimman ka'idoji 5 na zama tare cikin lumana', wadanda suke samun karbuwa sosai a tsakanin kasa da kasa a halin yanzu."

1 2 3