A yayin da yake zantawa kan nasarorin da Sin ta samu a fannin gudanar da harkokin diflomasiyya tare da bangarori daban-daban, Mista Yang ya ce, tun kafuwar sabuwar kasar Sin, musamman ma tun da aka soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje nan da shekaru 30 da suka shige, kasar Sin na kara taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban, ciki kuwa har da yin shiga-tsakani a manyan batutuwan shiyya-shiyya da na kasa da kasa, da kiyaye zaman lafiya a duniya da saurans. Yang ya furta cewa: "Kasar Sin na dukufa ka'in da na'in kan bin ka'idojin kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, da yin kokarin shawo kan rikicin duniya ta hanyar yin shawarwari da tattaunawa."
1 2 3
|