Ta la'akari da kin jinin juna da aka samu tsakanin kasar Libya da kasashen yamma cikin shekaru da yawa da suka wuce, da kuma takunkumin da MDD ta saka wa Libya, shugaba Gadaffi ya fara nuna saukin kai kan wasu matsaloli, kamar yadda gwamnatin kasar Libya ta sanar da cewa ta dauki alhakin haddasa hadarin jirgin sama na Lockerbie a shekarar 1988, sa'an nan ta biya wa iyalan fasinjojin jirgin diyya, abun da ya saukaka tsamin dangantakar da ke tsakanin Libya da kasashen yamma. Daga baya kuma, kasar Libya ta yi watsi da shirinta na binciken makaman kare dangi, ta hakan ta samu damar cire takunkumin da aka saka mata.
Sa'an nan kasar Libya ta sake taka rawa a dandalin kasa da kasa, inda ta fi mai da hankali kan huldar da ke tsakaninta da sauran kasashen Afirka. Wani babban burin kasar shi ne, ta zama wata babbar kasar da ke taka rawar a gani wajen daidaita harkokin nahiyar Afirka, sa'an nan ta kara habaka tasirinta kan kasashen duniya.
Ganin shugabannin kasashen Afirka da yawa sun halarci bukukuwan kasar Libya, ya sa masu binciken al'amuran duniya ke tsammanin cewa, abin ya nuna martabar da shugaba Gaddafi ke da ita a nahiyar Afirka, wadda za ta sa kasashen yamma su kara dora muhimmanci kan kasar Libya.(Bello Wang) 1 2 3
|