Cikin wadannan shekaru 40 da shugaba Gaddafi yake kan karagar mulki, bai samu matsayi mai kyau ba a idanun kasashen yamma, amma nasarorin da ya samu yayin da yake kula da harkokin gida sun sa ya samu kwarjini da martaba cikin zukatan jama'ar kasar Libya, in ji Sun Lizhou, wani masanin kasar Sin da ke binciken huldar kasa da kasa.
Bayan da aka tumbuke mulkin sarakuna, an kafa jamhuriya a kasar Libya, inda aka rungumi tsarin siyasa na zamani. Sa'an nan wajen tattalin arziki, zaman rayuwar jama'ar kasar Libya ya gyaru sosai. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Libya na kokarin daukaka matsayinta a duniya, bisa dimbin albarkatun kasa da Allah ya huwace wa kasar, da kuma daukan nagartattun matakan diplomasiyya.
1 2 3
|