
Wani dattijon kauyen mai suna August Brandenburg ya furta cewa: "An soma ayyukan gina kauyen Juhnde mai samar da makamashi irin na halittu ne a ranar 27 ga watan Satumba na shekarar 2005. amma kafin wannan lokaci, Jami'ar Gottingen ta yi ta yin kokarin samun wata hanya ta daban don bunkasa sha'anin noma. A karshen dai, Jami'ar din ta tsaida kudurin zaben kauyuka 17 daga 21 na yankin Gottingen don yin gwajin samun mamashi irin na halittu".
Jama'a masu sauraro, a zahiri dai, gina kauye mai samar da makamashi irin na halittu da aka yi tare da nasara, ba ma kawai ya kiyaye albarkatun ma'adinai ba, wadanda sai kara raguwa suke a kowace rana, har ma ya rage fitar da kashi 60 cikin 100 na iskar ' Carbon-Dioxide'.
A karshe dai, Mista Fangmeier ya furta cewa: "Lallai an ci nasarar bin salo irin na kauyen Juhnde. Amma mutanen kauyen suna da wata babbar manufa ta nan gaba, wato ke nan za su yi namajin kokari wajen samun sabbin makamashi daga hasken rana'.( Sani Wang ) 1 2 3
|