Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-27 14:20:05    
Rangadin gani da ido a shahararren kauye mai samar da makamashi irin na halittu a Jamus

cri

Mista Eckhard Fangmeier, mamban kwamitin sa ido kan harkokin kamfanin ya fada wa wakilinmu cewa: "Na yi alfarmar gina wani kauye na farko mai samar da makamashi irin na halittu. Lallai an samu manyen sauye-sauye bayan kafuwar hadadden kamfanin, wanda ya kasance kauye na farko mai samar da makamashi irin na halittu a kasar Jamus da ma duk Nahiyar Turai. Kuma daukacin mutanen kauyen sun samu ilimi mai zurfi a fannin zaman-takewar al'umma da kuma kiyaye muhalli".

Kauyen Juhnde na da gonaki masu fadin kadada 1,300 da kuma gandun daji mai fadin kadada 800; kuma kadada 250 daga cikinsu, ana amfani da su ne don shuka amfanin gona, ta yadda za su samu makamashi irin na halittu. Ban da wannan kuma, mutanen kauyen sun yi renon shanu kusan 800 masu bada nono da kuma aladai 2,000. A shekarar 2008, mutanen kauyen sun samu wutar lantarki da karfinsu ya kai kilo-watts miliyan 5 daga kashin dabbobi da yawansu ya kai ninkin-mita 9,000 da kuma barbashin amfanin gona da nauyinsu ya kai Ton 12,000 bayan an ruba su da kuma kona su yayin da aka samu makamashin zafi da yawansu ya kai kilo-watts miliyan 4, wadanda suka biya bukatun dukannin mutanen kauyen na kilo-watts miliyan 2.

1 2 3