Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-26 17:09:56    
Gardama na kara tsanani kan zaben shugaban kasa a Afghanistan

cri

Masu bincike sun yi nuni da cewa, saboda takkadama mai tsanani da ake yi, jama'ar kasar Afghanistan sun nuna damuwa kan hakan zai iya wannan zai haddasa rikicin nuna karfin tuwo. Ban da haka kuma, Karzai da Abdullah su wakilai ne na kabilar Pushtun da na kabilar Tajik, watakila wannan takkadama za ta tsananta yanayin da Afghanistan ke ciki.

Ban da haka kuma, dakarun kungiyar Taliban suna ci gaba da kai hare-hare. Bayan da aka sanar da sakamakon zabe a karo na farko, an kai harin kunar bakin wake ta hanyar tayar da boma boman da aka dasa cikin mota, mutane fiye da 40 sun mutu, wasu mutane fiye da 80 sun jikkata.

Masu bincike suna ganin cewa, duk wanda ya yi nasara a babban zabe a yanayin "nuna karfin tuwo da jayayya" da ake ciki, kalubale mafi girma shi ne yadda zai iya warware jayayya da mayar da halin da ake ciki ya zauna da gindinsa cikin sauri. [Musa Guo]


1 2 3