A wannan rana, Mr. Richard C. Holbrooke manzon musamman na kasar Amurka mai kula da harkokin kasar Afghanistan ya nuna cewa, sakamako a karo na farko ba sakamako ne na karshe ba, yanzu ba lokacin yin tattaunawa kan sakamako na karshe ba ne.
Masu bincike suna ganin cewa, ko da yake yawan kuri'un da Karzai da Abdullah suka samu suna kusantar juna a yanzu, amma daga cikin kuri'u kashi 10 da aka kidaya, yawancinsu daga yankin arewancin kasar Afghanistan inda masu goyon bayan Abdullah ya fi yawa, amma har zuwa yanzu, ba a kidaya kuri'u a yankunan da dama masu goyon bayan Karzai suka fi yawa ba. Bisa ci gaban aikin kidaya kuri'u, yawan kuri'un da Karzai ya samu zai ci gaba da karuwa sosai. Ban da haka kuma, bisa kididdigar da aka yi, yawan mutanen da suka jefa kuri'a cikin babban zabe na wannan karo ya kai kashi 35 cikin kashi 100 kawai, wannan ya kasa da kashi 70 cikin 100 na shekarar 2004 lokacin da aka yi babban zabe a karo na farko.
Yanzu, ana ci gaba da gardama kan magudin da aka samu cikin zaben. Ran 25 ga wata, 'yan takara 6 ciki har da Ghani tsohon ministan harkokin kudi sun bayar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi tababa kan adalci cikin zaben. Kafin hukumar zabe ta bayar da sakamakon kidaya kuri'u a karo na farko, Abdullah ya ce, "ba shakka, an yi magudi mai yawa", kungiyarsa mai kula da yin zabe ta riga ta gabatar da kararraki fiye da 200 ga hukumar zabe. Ya nuna cewa, ba zai karbi sakamakon zabe tattara da magudi ba. Wani 'dan takara daban Mirwais Yasini ya ce, kungiyarsa mai kula da yin zabe ta sami watsin kuri'u fiye da 800 na goyon bayansa da aka yi. Bisa labarin da muka samu, an ce, hukumar daukaka kara ta babban zabe a kasar Afghanistan ta riga ta karbi kararraki fiye da 800, kuma tana yin bincike kan wadannan kararraki.
1 2 3
|