Tun bayan shekarar 2006 a yankin Neja Delta, kungiyar dakaru mai adawa da gwamnatin Nijeriya ta kai hare-hare da dama tare da gudanar da danyun ayyuka, wadanda suka yi sanadiyyar jerin raguwar man fetur da aka fitar a Nijeriya. Don haka, gwamnatin Amurka ta mai da hankali sosai kan yanayin tsaro da ake ciki a wannan yanki, tare da nuna damuwa cewa, tabarbarewar yanayin za ta yi illa ga aikin samar da man fetur ga Amurka da Nijeriya take yi. A sakamakon haka, Amurka ta fara neman sabbin kasashe masu samar da makamashi, kamar Angola, tare da sa kaimi ga gwamnatin Nijeriya da ta kawo karshen rikicin Neja Delta cikin sauri. Kuma ta bayyana fatanta na ba da gudummawa ga Nijeriya kan lamarin.
Wasu manazarta sun kyautata zaton cewa, watakila Amurka za ta sa hannu a rikicin Neja Delta, a yunkurin tabbatar da samarwar man fetur da kiyaye moriyar kamfanonin man fetur na Amurka a Nijeriya. Duk da haka, gwamnatocin kasashen biyu za su yi shawarwari kan hanyar kutsa kai da Amurka za ta bi. Amma wasu manazarta sun yi zaton cewa, watakila nuna ra'ayin da Clinton ta yi a yayin ziyara a Nijeriya dangane da hadin gwiwa a fannin aikin soja a yunkurin daidaita rikicin Neja Delta zai yi illa ga aikin yiwa dakaru afuwa da ake gudanar. Mai yiwuwa dakaru za su yi tsammani cewa, yi musu afuwa wani makirci ne kawai da gwamnatin ta yi. Da karshe za ta daidaita rikicin Neja Delta da karfin soja bisa taimakon kasar Amurka.(Fatima) 1 2 3
|