Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-13 16:10:03    
Hillary Clinton ta mai da hankali kan yanayin tsaro a muhimmin yankin fitar da man fetur dake Nijeriya

cri

A gun taron manema labaru da aka shirya bayan shawarwarin, abu na farko da malam Maduekwe ya ambata shi ne batun tsaro a yankin Neja Delta. Ya bayyana cewa, umurnin yiwa dakaru masu adawa da gwamnati afuwa da gwamnatin Nijeriya ta bayar a kwanan baya ya riga ya fara aiki, a sakamakon haka, halin da ake ciki a wannan yanki ya sami kyautatuwa a bayyane. Ya kara da cewa kuma, shugaba Yar'Adua ya yi imani cewa, za a cimma nasarar farfado da zaman lafiya a yankin Neja Delta kafin karshen bana, tare da samun farfadowar aikin samar da man fetur.

A gun taron manema labaru, Hillary Clinton ta furta cewa, kokarin da gwamnatin Nijeriya ta yi na shawo kan rikici a yankin Neja Delta ya kara kwarin gwiwar jama'a wajen sake shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki. Ta bayyana cewa, ministan tsaron kasar Nijeriya ya gabatar da cikakkiyar shawara ga Amurka game da yadda za ta taimakawa Nijeriya wajen daidaita wannan matsala. Rundunonin soja na kasashen biyu za su yi karin shawarwari kan lamarin. Hillary Clinton ta furta cewa, rundunonin soja na kasashen biyu suna da kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa, a sakamakon haka, Amurka za ta baiwa gwamnatin Nijeriya taimako wajen daidaita rikicin tsaro da aka samu a kasar.

Kowa ya sani, man fetur muhimmin abu ne dake hada Amurka da Nijeriya. A shekarar 2008, a kowace rana Nijeriya ta kan fitar da man fetur na ganga miliyan 1.05 ga Amurka, wato tana kan matsayi na biyar wajen samar da man fetur ga Amurka. Shi ya sa kafin isowar Hillary Clinton a Nijeriya, mataimakin sakataren harkokin waje na Amurka Johnnie Carson ya bayyana cewa, ba shakka Nijeriya wata kasa ce mafi muhimmanci a Afirka dake kudu da sahara, sabo da haka ne gwamnatin Barack Obama ta yi fatan karfafa dangantaka tsakaninta da Nijeriya. Bugu da kari, yayin da take ganawa da jami'an Nijeriya, Hillary Clinton ta kira Nijeriya "aminiya" da "abokiyar hadin gwiwa a fannoni da yawa".

1 2 3