Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-12 13:26:08    
Hillary ta kalubalanci gwamnatin Kongo Kinshasa da ta kare 'yan mata don kada a ci zarafinsu

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar na nuna cewa, akwai 'yan mata akalla 200,000 ne da aka yi musu fyade a lardin Kivu dake gabashin kasar Kongo Kinshasa tun bayan abkuwar rikice-rikicen soji tsakanin sojojin gwamnatin kasar da kuma kungiyoyin 'yan tawaye masu yin adawa da gwamnatin kasar a shekarar 1996. Yake-yaken basasa da suka ki ci suka ki cinyewa suka sa wannan yanki ya zama daya daga cikin wuraren da suka fi talauci a fadin duk duniya, inda miliyoyin jama'a suka shiga cikin halin balagaita.

Daga nan ne ake ganin cewa, halin tangal-tangal da ake ciki yanzu a wannan yanki, shi ne muhimmin dalilin haifar da dimbin matsalolin cin zarafin 'yan mata. Kuma sanadin rashin tabbas din yanayin tsaro na wannan yanki shi ne kasancewar albarkatun ma'adinai masu yawan gaske a can, inda gwamnatin kasar Kongo Kinshasa da kuma dakarun sojojin da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar dake tsugunewa a can suke hakar ma'adinan wurin don sayar da su zuwa kasashen ketare da zummar sayen makamai.

1 2 3