A wani bangare na daban kuma, kasashen yammacin duniya, ciki har da wadanda suka taba yin mulkin mallaka sun ba da babban tasiri a Madagascar. Ko da yake tun daga shekatun 1950, kasashen Afirka sun soma samun 'yancin kai daya bayan baya, sun kau da mulkin mallaka da kasashen yammacin duniya suka yi musu, sun raunana tasirin 'yan mulkin mallaka, amma 'yan mulkin mallakar ba su daina yin tasiri gare su ba.
Manazarta sun nuna cewa, ko da yake yau shekaru 50 ko fiye da suka wuce, kasashen Afirka sun samu 'yancin kai a harkokin siyasa, amma suna fuskantar jan aiki wajen kau da tasirin 'yan mulkin mallaka. Musamman ma a harkokin tattalin arziki, ya zuwa yanzu yawancin albarkatun ma'adinai da yankunan kasa da kasashe da yawa na Afirka suke mallaka na cikin hannun kasashen da suka taba yi musu mulkin mallaka, dan haka wadannan kasashen Afirka ba su iya samun cikakken iko ta fuskar siyasa ba. Wannan shi ne daya daga cikin manyan dalilan da suka sa a kasashen Afirka suka samu rikicin siyasa. In ba a canza irin wannan hali ba, to, da wuya sosai a samu kwanciyar hankali ta fuskar siyasa a Madagascar har abada.(Tasallah) 1 2 3
|