A sakamakon matsin lamba daga kasashen duniya, a ran 5 ga wata, mutane 4 da suke da babban tasiri a hakikanin harkokin siyasa a Madagascar wato shugaban hukumar iko ta wucin gadi ta koli Andry Rajoelina da tsoffin shugabannin kasar Marc Ravalomanana da Didier Ratsiraka da Albert Zafy sun yi shawarwari a sakamakon kokarin da tsohon shugaban Mozambique Joaquim Chissano ya yi, wanda kungiyar tarayyar kudancin Afirka wato SADC ta nada shi a matsayin mai shiga tsakani. Sun sake himmantuwa wajen fita daga halin kaka-ni-ka-yi a harkokin siyasa.
Bayan da aka daddale yarjejeniyar sulhuntawa a hukumance a ran 9 ga wata da sassafe, yanzu kasashen duniya suna mai da hankali kan ganin yarjejeniyar ta taimakawa Madagascar ta sami kwanciyar hankali a harkokin siyasa har abada. Wannan kasa ta sha fuskantar juyin mulki a shekarun baya. Kuma a lokacin aukuwar wadannan juye juyen mulki, a kan samu tsananin rikicin siyasa da kuma tashe-tashen hankali.
Ina dalilin da ya sa aka sha yin juyin mulki a kasar Madagascar a shekarun baya? Dalilan cikin gida masu sarkakiyya su ne suka haifar da haka. Ko da yake an daddale yarjejeniyar sulhuntawa a tsakanin bangarori daban daban a Madagascar, amma da wuya ne sosai suka sami ra'ayi daya kan wasu muhimman batutuwa.
1 2 3
|