Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-11 16:56:29    
Madagascarr na fuskantar doguwar hanya ta samun kwanciyar hankali a harkokin siyasa

cri

A kwanan baya, a birnin Maputo, hedkwatar kasar Mozambique, an kawo karshen shawarwari na tsawon kwanaki 5 kan rarraba iko a tsakanin bangarorin kasar Madagascar, inda bangarorin suka daddale yarjejeniyar sulhuntawa da taswirar hanya ta wucin gadi. Ta haka an sa aya ga rikicin siyasa da wannan kasa ta yi watanni da dama tana fama da shi. Manazarta sun yi hasashen cewa, Madagascar na ci gaba da fuskantar doguwar hanya wajen samun kwanciyar hankali a harkokin siyasa har abada.

Bisa abubuwan da ke cikin wannan yarjejeniyar sulhuntawa, an ce, a cikin nan da watanni 15 masu zuwa, hukumar iko ta wucin gadi ta koli ta Madagascar za ta shugabanci da kuma kammala aikin yin gyare-gyare kan tsarin mulkin kasa, za ta kuma shirya babban zaben shugaban kasa. Marc Ravalomanana, tsohon shugaban Madagascar ya nuna cewa, domin samun moriyar kasarsa, ba zai shiga cikin ayyukan mika ikon mulkin kasar kai tsaye ba. A sa'i daya kuma, hukumar iko ta wucin gadi ta koli ta Madagascar za ta yi masa afuwa, za ta kuma amince da masa kawo karshen gudun hijira ta fuskar siyasa, inda zai iya koma gida.

Madagascar na daya daga cikin kasashe mafi rashin ci gaba a duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar. Tana dogara da aikin yawon shakatawa da kuma taimakon kasashen waje. Rikicin siyasa ya sanya yawancin matafiyan da suka fito daga kasashen waje su soke ziyararsu a Madagascar, kana kuma, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da yawa sun dakatar da ba ta taimakon tattalin arziki.

1 2 3