A cikin 'yan shekarun nan, sana'ar kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi ta zama daya daga cikin muhimman sana'o'in da kasashe daban daban suke kokarin raya su. Kasar Sin tana kuma mai da hankali sosai kan aikin nazari da kuma kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Sakamakon haka, ta samu babban ci gaban muhimman fasahohin kera motoci masu aiki da nau'o'in makamashi a cikin kusan shekaru 10 da suka gabata. A yayin bikin nune-nunen motoci na duniya da aka yi a kwanan baya, Mr. Miao Wei, mataimakin ministan kula da harkokin masana'antu da sadarwa na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta bullo da matakai da manufofi filla filla domin kara saurin samar da motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Mr. Miao ya ce, "Za mu kara saurin kafa sabbin ma'aunai game da kayayyaki mafi muhimmanci na motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Sannan za mu kara saurin kafa tsarin ba da sanarwa ga jama'a game da motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Bugu da kari kuma, za mu kara saurin kyautata wasu muhimman fasahohin kera irin wannan mota. Haka kuma, za mu kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin sana'o'i daban daban domin kowace sana'a za ta iya bayar da gudummawarta kamar yadda ya kamata. Sakamakon haka, za mu iya ciyar da sana'ar nazari da kuma kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi gaba."
A ganin kamfanonin kera motoci na duk duniya, kasuwar kasar Sin tana jawo hankalinsu sosai. A cikin 'yan shekarun baya, wasu manyan kamfanonin kera motoci na duniya sun kuma soma zuba jari kan ayyukan nazarin motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi a kasar Sin domin kokarin samun kasuwanci a kasar. Mr. Susan Cischke, mataimakin babban direkta mai kula da harkokin neman ci gaba ba tare da tangarda ba a sashen kamfanin Ford na kasar Amurka da ke nan kasar Sin ya bayyana cewa, kamfanin Ford zai samar da karin motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi a kasar Sin da sauran kasashen duniya. Mr. Cischke ya ce, "Yau da shekaru 2 da rabi da suka gabata, mun tsai da kudurin cewa, dole ne mu kera motoci masu tsimin man fetur. Sabo da haka, mun mai da hankali kan yadda za a yi tsimin man fetur a cikin motoci masu shan mai da man gas. A waje daya, mun mai da hankali wajen nazari da kuma samar da motoci masu aiki da wutar lantarki da motoci masu aiki da nau'o'in makamashi iri daban daban da motoci masu aiki da batir. A nan gaba, za mu samar wa kasuwar kasar Sin irin wadannan motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi a kai a kai."
Bisa tallafin gwamnati da halartar kamfanonin kera motoci da goyon bayan da jama'a suke nuna wa kokarin kiyaye muhalli, ana sa ran cewa, makomar motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi tana da kyau. Mr. Fu Yuwu, babban sakataren kungiyar aikin injiniya na motoci ta kasar Sin ya ce, "Irin wadannan motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi za su samu karuwa sosai a nan gaba."
Masana sun nuna cewa, yanzu fasahohin nazari da kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi da kasar Sin ta mallaka suna kusan daidai da na kasashe masu ci gaba. Idan masana'antun kera motoci na kasar Sin sun kara mai da hankali wajen yin nazarinsu da kuma kyautata ingancin motocinsu da kuma hidimarsu, tabbas ne sana'ar kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi za ta samu ci gaba, kuma tana da makoma mai kyau sosai a kasar Sin. (Sanusi Chen) 1 2 3
|