A kwanan baya, kamfanin motoci na Foton na Beijing ya kulla yarjejeniyar sayar wa kamfanin motoci na Chengyun na Taiwan motoci 75 masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Wannan ne karo na farko da wani kamfanin babban yankin kasar Sin ya sayar wa kamfanin Taiwan motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Yau da shekara daya da ta gabata, kamfanin Foton ya taba sayar wa wani kamfanin motocin bas da ke birnin Guangzhou irin wadannan motoci.
A ganin Zhao Jingguang wanda ke kula da harkokin kamfanin Foton, idan motocin masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi suna son samun kwangila a kasuwa, dole ne suna da sharuda mafi rinjaye. Mr. Zhao ya ce, "Kamfanin motocin bos na Guangzhou ya gwada yin amfani da irin wadannan motoci. Bayan rabin shekara, za a duba yawan man fetur da aka yi tsimi, da kuma yawan gurbatattun abubuwan da irin wadannan motoci suka fitar. Bayan sun samu irin wadannan adadi, za su tsai da kudurin ko za su sayi motocinmu ko ba za su saya ba."
Bayan da kamfanin motocin bas na birnin Guangzhou ya yi shekara 1 yana amfani da irin wadannan motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi, an samu sakamako mai kyau. Idan an kwatanta motocin da aka saba amfani da su, yawan man fetur da aka yi tsimi ya kai kashi 1 cikin kashi 4. Sakamakon haka, yawan kudin da aka yi tsimi ya kai kudin Sin yuan dubu 90 a cikin shekara 1. Sabo da haka, jimillar kudin da za a yi tsimi zai kai kudin Sin yuan dubu dari 7 cikin shekaru 8, wato wa'adin aikin kowace motar bas. A waje daya, yawan abubuwan dumama yanayin duniya da za a rage fitarwa zai kai ton 27.
1 2 3
|