Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-11 16:17:16    
Masana'antun motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi suna da makoma mai kyau

cri

Ya kasance tamkar sansanin kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi a babban yankin kasar Sin, kamfanin motoci na Foton na Beijing ya soma yin nazarin motocin masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi tun daga shekara ta 2003. Ya zuwa yanzu, ya riga ya samu nasarar kera motoci masu aiki da nau'o'in makamashi iri daban daban. Musamman ya samu ci gaba sosai wajen yin amfani da batura iri daban daban a cikin motocin da ya kera. Alal misali, a yayin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing da aka yi a bara, ya samar da dimbin motoci masu aiki da batura ga gasar domin sufurin 'yan jarida da 'yan kallo da 'yan wasannin motsa jiki. Har yanzu irin wadannan motoci suna aiki a nan birnin Beijing domin sufurin fasinjoji a kowace rana.

Ba ma kawai kamfanin motoci na Foton na Beijing yana nazarin kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi ba, har ma sauran kamfanonin motoci da yawa suna nazarin irin wadannan fasahohin yin amfani da sabbin nau'o'in makamashi mai tsabta, kuma suna kokarin sayar da sabbin motocinsu a kasuwa.

A watan Yuni na shekarar da ake ciki, kamfanin motoci na BYD na kasar Sin ya samar wa birnin Shenzhen wasu motoci masu aiki da sabon nau'in makamashi ta fasahar F3DM bisa kwangilar da ya kulla da gwamnatin birnin Shenzhen. An bayyana cewa, bayan da batur na irin wannan mota ya sake samun karfi, mota za ta iya gudu har tsawon kilomita dari 1 a kowane karo. Yawan kudin da za a kashe ba zai kai kudin Sin yuan 10 ba, wato ba ma kawai ba za a fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ba, har ma za a yi tsimin kudi sosai. Kamfanin motoci na BYD shi da kansa ne ya mallaki fasaha mafi muhimmanci ta kera irin wannan mota. Mr. Xu An wanda ke kula da harkokin cudanya da jama'a a kamfanin motoci na BYD ya gaya wa wakilinmu cewa, wasu sanannun kamfanonin kasashen waje sun soma tuntubar kamfaninsu domin neman damar yin hadin gwiwa sakamakon matsayin rinjaye da kamfanin BYD yake dauka. Mr. Xu ya ce, "A kwanan baya mun kulla wata takardar fahimtar juna da kamfanin Volkswagen na kasar Jamus domin kara yin hadin gwiwa a fannin nazarin kera motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi. Yanzu, motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi da muka kera sun riga sun jawo hankalin mutane sosai, kamar wasu kamfanonin kera motoci da suka yi suna sosai a duk duniya. Muna kuma fatan za mu iya yin hadin gwiwa da wadannan kamfanoni domin kokarin samun ci gaba a fannin samar da motoci masu aiki da sabbin nau'o'in makamashi."

1 2 3