|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2009-08-10 20:30:26
|
 |
Kasar Sin ta shirya taron tattaunawa don tunawa da ranar cika shekaru 20 da rasuwar Burhan al-Shahidi
cri
 A farkon shekaru 50 na karnin da ya wuce, Burhan ya taba cewa, 'tilas ne mu kiyaye sada zumunta da hadin kai tsakanin kabilu daban daban kamar kiyaye rayuwarmu da idanunmu.' Yanzu, wannan magana ta riga ta zama wani tunanin da ake yaduwa tsakanin mabiyan addinin musulunci, da musulmai. A gun taron tattaunawa kuma, Erie Su-Ya, 'Yar Burhan ta waiwayo cewa, 'Ubana ya taba gaya mini cewa, ya kamata mu yi la'akari da kiyaye moriyar kabilu daban daban a lokacin da muke aikace-aikace, amma ba mayar da hankali kan moriyar kabilarmu kawai ba.'
Masu halartar taron sun bayyana cewa, a karkashin kokarin da Burhan, da kuma sauran 'yan kishin kasa suka yi, jihar Xinjiang ta samu nasarori da yawa a fannoni daban daban, amma 'yan a-ware ba su yi watsi da ra'ayinsu na balle Xinjiang daga kasar Sin. Saboda haka, har zuwa yanzu, kyakkyawan tunani na Burhan na neman gaskiya, da adawa da 'yan a-ware, da kiyaye hadin kai na da ma'ana sosai. 1 2 3
|
|
|