Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-10 20:30:26    
Kasar Sin ta shirya taron tattaunawa don tunawa da ranar cika shekaru 20 da rasuwar Burhan al-Shahidi

cri

A ranar 10 ga wata a nan birnin Beijing, ma'aikatar kula da harkokin dunkulalliyar kungiyar gwagwarmaya ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, da kwamitin jam'iyyar na jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta Uygur sun yi taron tattaunawa, don tunawa da cika shekaru 20 da rasuwar Burhan al-Shahidi, 'dan kishin kasa na kabilar Uygur a jihar Xinjiang.

Burhan, wani shahararren 'dan kishin kasa, kuma 'dan gwagwarmayar al'umma na kabilar Uygur, ya taba zama mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma shugaba mai daraja na majalisar Musulunci ta kasar Sin. Ya taka muhimmiyar rawa kan kiyaye cikakken yankin kasa, da inganta yunkurin tabbatar da zaman lafiya da 'yantar da jihar Xinjiang. A shekaru 40 na karnin da ya wuce kuma, akwai 'yan a-ware da suka nemi kafa kasar Turkistan ta gabas a jihar Xinjiang. A matsayinsa na shugaban jihar Xinjiang ta gwamnatin al'umma a wancan lokaci, Burhan ya yi amfani da ilmin tarihi mai yawa don yaki da 'yan a-ware. Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar jihar Xinjiang Ashat Kerimbay ya waiwayo a gun taron tattaunawa da aka shirya a wannan rana cewa, 'A karshen shekarar 1948, wasu 'yan a-ware ba su sasanta ba sun kuma kasa samu sa'a wajen samun 'yancin kan Turkistan ta Gabas, Burhan ya yi yaki tare da mutanen Turkistan ta Gabas. Bayan haka kuma, ya yi amfani da ilmin tarihi da ya samu don bayyana asalin Turkistan ta Gabas, da kuma dangantaka tsakanin jihar Xinjiang da kasar haihuwa.'
1 2 3