Dangane da matsalar hada-hadar kudi dake addabar dukkanin duniya, Sin da Amurka suna iya kara cimma moriyar juna. Kamar yadda mataimakin firaministan kasar Sin Mista Wang Qishan ya nuna cewa a yayin shawarwarin, kamata ya yi bangarorin biyu su inganta manufofin daidaita tattalin arziki daga manyan fannoni, da tabbatar da dorewar kafofin hada-hadar kudi, da yin kokarin farfado da tattalin arziki, gami da samar da karin guraben ayyukan yi. Ban da wannan kuma, akwai fannoni da dama wadanda kasashen Sin da Amurka kamata ya yi su karfafa hadin-gwiwa da cimma daidaito a kansu, ciki kuwa har da yin gyare-gyare ga tsarin tattalin arziki, da kara hadin-kai a fannonin yin kwaskwarima ga harkokin bada jiyya da kiwon lafiya, da kafa wani ingantaccen tsarin hada-hadar kudi, ta yadda za'a bada tabbaci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa.(Murtala) 1 2 3
|