Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-30 18:00:47    
Inganta huldodin kasashen Sin da Amurka ta fuskar cimma moriyar juna a karni na 21

cri

Abun da ya fi jawo hankali shi ne, kasashen Sin da Amurka sun daddale takardar bayani kan inganta hadin-gwiwa a fannonin tinkarar sauyin yanayi, da harkokin makamashi da kiyaye muhallin halittu. Akidar neman bunkasuwa ta fasaha daga dukkanin fannoni, muhimmiyar manufa ce da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa a kai domin neman samun karin ci gaba. A nasa bangare kuma, shugaban Amurka Barack Obama zai inganta aikin raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba zuwa matsayin wani muhimmin tsari, wanda ke shafar makomar kasar. Hakan na nuna cewa, kasashen Sin da Amurka sun samu ra'ayi kusan iri daya a manyan tsare-tsaren dake shafar makomarsu.

Dadin dadawa kuma, a matsayin kasar dake tasowa mafi girma, da kasa mai ci gaban masana'antu mafi girma a duniya, Sin da Amurka suna fuskantar kalubaloli a fannonin yin tsimin makamashi, da yin amfani da makamashin bola-jari, da tinkarar sauyin yanayi da dai sauransu. A nasa bangare kuma, mataimakin darektan kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin, wanda ya halarci taron shawarwarin, Mista Xie Zhenhua ya bayyana cewa, a yayin taron, kasashen Sin da Amurka sun bayyana kyakkyawan fatansu na karfafa hadin-gwiwa a wadannan fannoni, haka kuma sun kara fahimtar juna a fannoni da dama.

1 2 3