Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-29 16:45:21    
Ya kamata kasar Amurka ta kara yin hakuri, in ji bangaren Isra'ila

cri

Amma, duk da cewa kasar Amurka tana neman sassanta damuwar kasar Isra'ila kan Iran, ba a ga alamar kawar da rikicin da ya kasance a tsakanin Amurka da Isra'ila dangane da batun gina matsugunan Yahudawa ba. A wannan karo, ma iya cewa, George Mitchell, manzon musamman na kasar Amurka kan batun gabas ta tsakiya, ya yi kai-komo a zirin gabas ta tsakiya don kai ziyara ga kasashe da dama, wadanda suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Syria, da Isra'ila, da kuma Masar. Sa'an nan a yammacin ranar 27 ga watan Yuli, ya yada zango a yankin Falasdinu, inda ya yi ganawa da Faisal Fayez, firayin minista na gwamnatin wucin gadi ta Falasdinu, da Mahmoud Abbas, shugaban hukumar ikon al'ummar Falasdinawa. Har yanzu bangaren Falasdinu bai canza manufarsa ba, wato muddin dai kasar Isra'ila ba ta daina aikinta na gina matsugunan Yahudawa ba, to, bangaren Falasdinu ba zai amince da komawa teburin shawarwari da Isra'ila ba. Sa'an nan a ranar 28 ga watan Yuli Mista Mitchell ya koma kasar Isra'ila, inda ya yi hira da Benjamin Netanyahu, firayin ministan kasar Isra'ila. Sai dai ba a samu takamaiman ci gaba ba a wajen tattaunawar da suka yi dagane da batun gina matsugunan Yahudawa. Cikin sanarwar da ta fito daga ofishin firayin ministan kasar Isra'ila, an ce, an nuna ra'ayi mai yakini a wajen tattaunawar tsakanin Mista Mitchell da Mista Netanyahu, amma ba a yi bayani kan abubuwan da aka tattauna a kai ba. Game da batun, manazarta na ganin cewa, watakila ana bukatar ci gaba da yin shawarwari har sau da yawa a tsakanin kasar Amurka da ta Isra'ila, ta yadda za a samu damar cimma matsaya daya kan batun gina matsugunan Yahudawa. (Bello Wang)


1 2 3