Idan an duba wuraren da Mista Gates da Mista Mitchell suka yada zango, za a ga alamar cewa, kasar Amurka tana so ta lallashi kawarta, kasar Isra'ila wadda ke damuwa kan maganar nukiliya na kasar Iran, kafin ta matsa mata lamba kan batun gina matsugunan Yahudawa. A ranar 27 ga watan Yuli, Robert Gates, ministan tsaron kasar Amurka, ya gana da takwaransa na kasar Isra'ila, Ehud Barak, da Benjamin Netanyahu, firayin ministan kasar Isra'ila, inda ya nanata ra'ayi daya da kasashen 2 suke da shi kan maganar nukiliyar kasar Iran, haka kuma, ya ce, shawarar da kasar Amurka ta samar wa kasar Iran ta warware maganar nukiliya ta hanyar diplomasiyya tana tare da wani wa'adi. Mista Gates ya kara da cewa, idan kokarin da ake yi wajen yin shawarwari ya bi ruwa, mai yiwuwa ne kasar Amurka za ta shawarci MDD don ta kara sanya wa kasar Iran takunkumi.
1 2 3
|