Wadannan wasannin kwaikwayo biyu su ne "Eugen Onegin" da Tchaikovsky ya tsara da kuma "Rayuwar kwararre a fannin wasannin fasaha" da mai tsara kide-kide na kasar Italiya Giacomo Puccini ya tsara. Daga bisani, Guo Shuzhen ta kan nuna wadannan wasannin kwaikwayo biyu a kasashen waje da kasar Sin, ta samu karbuwa sosai. Yanzu, bari mu saurari wakar da Guo Shuzhen ta rera a cikin wasan kwaikwayo mai suna "Eugen Onegin". To, ga ta.
Bayan da Guo Shuzhen ta dawo kasar Sin, ban da aikin rera wakoki, haka kuma ta zama malama a jami'ar koyon ilmin kide-kide ta tsakiyar kasar Sin don koyar da fasahar rera waka da wasan kwaikwayo, ta horar da kwararru a fannin rera wakoki da yawa a cikin goman shekaru. Ya zuwa yanzu, ta horar da dalibai fiye da goma.
Dalibanta sun ce, sun yi sa'a sun iya koyon fasahar rera wakoki daga malama Guo Shuzhen. Wani dalibarta mai suna Zhang Jiajia ta ce, "Malama Guo ta tsaurara horar da dalibai sosai. Ta koyar da ilmin fasahar rera wakoki da yin nune-nune a fannoni da yawa. Mun yi sa'a sosai mun dora muhimmanci sosai kan darasin da ta bayar."
A ran 10 ga wata, an yi bikin kide-kide na daliban Guo Shuzhen a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin don taya murnar cika shekaru 62 da Guo Shuzhen ta fara zama malama.
Malama Guo Shuzhen ta ce, a cikin goman shekarun da suka wuce, na koya wa dalibai ilmi, a sa'i daya, ni ma na azurta rayuwata. 1 2 3
|