Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-29 15:31:47    
Kaddarar dake tsakanin shahararriyar mawakiyar kasar Sin Guo Shuzhen da kasar Rasha

cri

Shekarar bana shekara ce ta harshen Rasha a kasar Sin, za mu gabatar muku wata shahararriyar mawakiyar kasar Sin Guo Shuzhen, wadda ke da shekaru 82 da haihuwa. A yayin da take a matashiya, an tura ta zuwa kasar Rasha, wato daga nan ne ta samu tasiri sosai daga kasar Rasha. Da farko, bari mu saurari wata waka mai suna Rusalka da Guo Shuzhen ta rera.

An haifi Guo Shuzhen a shekarar 1927 a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin. Mahaifinta ya iya rubuta sunansa kawai, mahaifiyarta tana da kyakkyawar murya. Duk da cewar, iyalanta ba su da wadata, amma sun sanya muhimmanci sosai kan karatu da koyon ilmi, sun tura Guo Shuzhen zuwa makaranta tare da fatan 'yarsu za ta nuna bajinta. Amma abin da ba su yi tsammani ba shi ne, a yayin da Guo Shuzhen ta shiga jami'a, ta yi niyyar karatu a jami'ar wasannin fasaha ta kasar Sin a birnin Beijing. A kasar Sin na wancan zamani, an yi biris ga mawaka da 'yan wasannin fasaha. Amma Guo Shuzhen ta tsaya kan ra'ayinta sosai. Ta ce, "Ina son rera wakoki sosai, birnin Tianjin birnin yin cinikayya ne, dukkan kantuna sun yi forfoganda kan kayayyakinsu ta lasfika. Su kan gabatar da wasannin kwaikwayo da kide-kide da wake-wake. Ina da kyakkyawar murya, kuma ina son rera wakoki. Na fara koyon ilmin kide-kide a yayin da nake karatu a aji na hudu a makarantar firamare. Malamar da ta koyar da ilmin kide-kide ta kan nuna yabo gare ni."

A shekarar farko da na cimma jarabawar shiga jami'ar wasannin fasaha, mahaifinta bai yarda 'yarsa ta yi karatu ilmin kide-kide. Amma a shekara ta biyu, Guo Shuzhen ta sake shiga jarabawar wannan jami'a, malamai sun gan ta, sun yi mamaki, sun tuna da wannan budurwa wadda ta cimma jarabawarsu a da. Bayan da malaman sun fahimci dalilin da ya sa Guo Shuzhen ba ta shiga jami'a ba, sun amince da karbar Guo Shuzhen kai tsaye. A karshe dai, mahaifin Guo Shuzhen ya yarda ta shiga jami'ar bayan da danginta suka lallashe shi.

1 2 3