Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-29 15:31:47    
Kaddarar dake tsakanin shahararriyar mawakiyar kasar Sin Guo Shuzhen da kasar Rasha

cri

A cikin jami'ar, malamar Guo Shuzhen ta farko ita ce wata mawakiyar Amurka, sannan ta koyi rera wakoki daga Zhao Meibo, shahararren 'dan wasan fasaha na kasar Sin wanda ya taba koyon ilmin rera wakoki a Turai, Guo Shuzhen ta aza harsashi ga fasaharta ta rera wakoki a nan.

A shekarar 1953, gwamnatin kasar Sin ta tura daliban matakin farko zuwa kasar Rasha don koyon ilmin rera wakoki da yin zane-zane, Guo Shuzhen ita ce daya daga cikinsu. A cikin shekaru biyar da Guo Shuzhen take karatu a jami'ar Tchaikovsky Conservatory ta Moscow, ta kara yin kokarin karatu. Guo Shuzhen ta waiwayi cewa, suna da darussa a kwanaki 6 a wani mako, malami ya ba ta aikin gida wato dauka wata rubutacciyar kida mai wuya a cikin zuciyata a wancan rana da dare, Guo Shuzhen ta kammala wannan aikin gida mai kyau, malaminta ta yi mamaki ta yaba ta a kashegari, sabo da ya san yadda Guo Shuzhen ta yi kokarin aiki.

Sabo da basirarta da kuma kokarin da ta yi, Guo Shuzhen ta samu sakamako mai kyau cikin sauri. A shekarar 1957, a cikin gasar rera wakokin gargajiya ta matasa ta birnin Moscow, Guo Shuzhen ta zama zakara bisa wakar Romantic da Achille-Claude Debussy ya tsara. Wato ke nan Guo Shuzhen ta ba joji-joji mamaki sosai. Guo Shuzhen ta ce"Wannan ne gasar da ta fi girma ta fannin rera wakoki. Galibin joji-joji su mutanen kasar Italiya ne."

Wannan ne karo na farko da wata Basiniya da ta zama zakara a gasar rera wakoki ta kasa da kasa, Guo Shuzhen ta shahara sosai a kasar Sin. Guo Shuzhen ta ce, a wancan lokaci, 'yan jaridu sun yi wa iyalanta intabiyu sau da yawa. Haka kuma, jami'ar Guo Shuzhen ta ba ta lambar yabo.

A lokacin da ta gama karatu a kasar Rasha, daliban ajinta sun dawo kasar Sin, amma Guo Shuzhen ta ci gaba da rera wakoki a kasashen gabashin Turai har na tsawon watanni shida, ta kara samun bunkasuwa a fannin fasahar rera wakoki. Guo Shuzhen ta kara da cewa, "Bayan shekaru biyar da na yi karatu a kasar Rasha, malamana sun tura ni zuwa kasashen kungiyar tarayyar Soviet don rera wakoki, wannan ya zama wata kyauta da kasar Rasha ta bai wa kawarta kasar Sin. Na zama jaruma a cikin wasannin kwaikwayo biyu."

1 2 3