Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-28 20:48:02    
Tabkin Xihu da ke birnin Hanzhou, aljanna ce a duniyarmu

cri

Tun daga ran 1 ga watan Mayu na shekarar bara, hukumar birnin Hangzhou ta rarraba kekuna fiye da dubu 2 a cibiyar birnin da wuraren yawon shakatawa. Ba a bukatar biyan kudi a cikin rabin awa. Bayan awa guda, ana bukatar biyan yuan 2. Matafiya suna iya yin hayar wadannan kekuna cikin sauki matuka. Da yawa daga cikinsu suna sha'awar irin wannan hanyar yin bulaguro ta zamani kuma ba tare da gurbata muhalli ba.

A bakin tabkin Xihu, mun gamu da Mr. Song, wani saurayi da ya fito daga lardin Jiangsu. A ganinsa, kewaya tabkin Xihu kan keke ba kawai ya iya samar wa matafiya sauki wajen jin dadin ganin kyan surar wannan tabki ba, har ma ya dace da ruhun 'shirya gasar wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba'. Yana mai cewar,"Irin wannan hanyar yin bulaguro tana iya kiyaye muhalli, amma ba a bukatar biyan kudi da yawa. A hakika, mu matasa mun iya motsa jikinmu. Yin hayar keke na da sauki da kuma rahusa sosai."

A karni na 13 da ya gabata, Marco Polo, wani shahararren matafiyi, dan kasar Italiya ya taba ambata birnin Hangzhou, wanda ke bakin teku a kudu maso gabashin kasar Sin, haka kuma, yana kuriyar kudu ta babbar koramar da ke tsakanin biranen Beijing da Hangzhou, tamkar birni mafi kyan gani a duk duniya. Masu suararo, wannan birnin da ya yi albarka a fannonin siliki, da shayin Longjing da aka samu a tabkin Xihu, da kifayen da aka dafa da bininga a bakin tabkin Xihu, da sauran abinci masu dadi kuma masu dogon tarihi zai iya ba ku damar jin dadin zaman rayuwa a aljannar da ke duniyarmu.

To, kafin mu kawo karshen shirinmu na yau, Yang Xiuping, wadda ta taba zama mai mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar bara, kuma tana tukin kwale-kwale a tabkin Xihu tana son yin maraba da matafiyan da suka fito daga sassa daban daban ta hanyar shirinmu. Madam Yang, bismila!


1 2 3