Yang Xiuping ta ja kwale-kwalenta zuwa madatsar ruwa ta Sudi. Su Dongpo, wani shahararren marubucin rubutattun wakoki na zamanin daular Song ya taba zama gwamnan Hangzhou. Ya gina wata madatsar ruwa tare da yin amfani da tabon da aka haka daga tabkin Xihu. Ta haka mazauna wurin sun saka wa wannan madatsar ruwa sunan wannan marubuci. Ma'anar Sudi ita ce madatsar ruwa da Su ya gina. A sakamakon kasancewar madatsar ruwa ta Sudi, an kara tsabtace ruwan wannan tabki. Bugu da kari kuma, ita kanta ta zama wani wurin yawon shakatawa na daban. An mayar da ita a matsayin ta farko a cikin wuraren yawon shakatawa mafi kyan gani guda 10 a tabkin Xihu.
Ko da yake yanzu lokacin zafi ya yi, lokacin bazara ya wuce. Amma a cikin ruwa mai launin kore, madatsar ruwa ta Sudi da aka samu itatuwa masu launin kore da furanni masu launuka daban daban a kai ta zama daya daga cikin wuraren yawon shakatawa da suka cancanci matafiya.
Bayan da aka yi gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar bara, sa'an nan kuma, za a yi taron baje-koli na kasa da kasa a birnin Shanghai a shekara mai zuwa, ma'aikatan hukumar yawon shakatawa ta tabkin Xihu a shirye suke, za su ba da kyakkyawan hidimomi ga matafiyan da suka fito daga sassa daban daban na kasar Sin gami da na duk duniya. Zhao Yuanchen yana tafiyar da harkokin wani shagon sayar da abubuwan tunawa ta fuskar yawon shakatawa a kusa da madatsar ruwa ta Sudi. Ma'aikatansa da shi dukkansu sun iya tuntubar baki cikin harsunan Turanci da Japananci da harsunan Korea ta kudu da Malaysia da sauran harsunan waje. Inda ya ce,"Baki da yawa kan kai ziyara a madatsar ruwa ta Sudi. Don ba da hidima mai kyau, da farko mun bukaci ma'aikatanmu su iya tuntubar baki cikin harsunan waje. In ba su san abubuwan da baki suka fada ba, to, ba za su iya gane su ba. Amma in mun iya harsunansu, za su iya gane cewa, jama'ar Sin suna kishin karbar baki. Haka kuma, wannan ya ba da taimako ga shagonmu."
Zhao Yuanchen ya ci gaba da cewa, baya ga sayen kyakkyawar laimar da mazauna tabkin Xihu suka yi da yin amfani da siliki da kuma fanka mai kamshi da aka iya ninkawa, matafiya kan kusanci tabkin Xihu ta wata hanya ta daban, wato kewaya wannan tabki kan keke.
1 2 3
|