Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-28 20:48:02    
Tabkin Xihu da ke birnin Hanzhou, aljanna ce a duniyarmu

cri

Yau ya rage sauran kwanaki dari 2 ko fiye a bude taron baje-koli na kasa da kasa na birnin Shanghai. Idan kun yi shirin zuwa birnin Shanghai a shekara mai zuwa, to, muna gabatar muku da wani ni'imtaccen wuri na daban, wato tabkin Xihu da ke birnin Hangzhou, wanda ke makwabtaka da Shanghai.

A watan Yuni da na Yuli na ko wace shekara, kamshin furannin lotus ya kan cika birnin Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang matuka. Sinawa su kan cewa, tabkin Xihu a lokacin tsananin zafi ya sha bamban da na sauran lokutan shekara. Kyan surarsa ta shiga cikin zukatan matafiya na gida da wajen kasar Sin.

A ko wace rana, jiragen kasa na kaiwa da kawowa a tsakanin birnin Shanghai da tabkin Xihu. A kan kwashe awoyi 2 ne kawai daga Shanghai zuwa wannan tabki. A ko wace shekara, matafiyan da suka fito daga sassa daban daban su kan kai ziyara a tabkin Xihu da zummar jin dadin kallon kyan surar wannan aljanna na rashin hayaniya.

An samu tabkin Xihu a cibiyar birnin Hangzhou. A can da, an taba kiran wannan tabki mai fadin murabba'in kilomita 5.66 kuma mai tsawon kilomita 15 da sunan 'Wulinshui' da na 'tabkin Qiantanghu' da na 'tabkin Xizihu'. Hanya mafi kyau da ake bi wajen kusantar tabkin Xihu ita ce tukin kwale-kwale a tabkin. Masu sauraro, in a karo na farko ne kuka shiga kwale-kwale a tabkin Xihu, to, muna gabatar muku da wata budurwa mai suna Yang Xiuping, wadda take tukin kwale-kwale a tabkin Xihu.

Yang Xiuping mai shekaru 30 da wani abu da haihuwa tana da kyan gani sosai ko da yake fatarta ta yi baki a sakamakon hasken rana. Ba ta kan fara tukin kwale-kwale ba sai matafiya sun zauna yadda ya kamata. Tare da amon da ruwa ke samarwa da kuma kukan tsutsotsin cicada da ke kan itatuwa a bakin tabkin, matafiya kan ji mamaki bisa kyan karkarar da suke gani, kuma wanda ya yi kama da zane-zane. Yang Xiuping ta gaya mana cewa,"Furannin lotus sun fi kyan gani a lokacin tsananin zafi. A dab da gada, ga furannin lotus masu yawa, ya fi kyau a dauki hoto tare da su. A duk shekara, tabkin Xihu kan nuna kyan surarsa. A lokacin bazara, a madatsar ruwa mai suna Sudi da ke dab da tabkin Xihu, ana iya ganin furannin peach. A lokacin zafi, ana iya ganin furannin lotus, a kaka kuwa, kallon wata a tabkinmu ya fi dacewa. Sa'an na kuma, in lokacin hunturu ya yi, jin dadin kallon kankara mai laushi da ke kan gadar Duanqiao kan faranta rayukan mutane."

Iska maras karfi na bugawa, shi ya sa babu babbar igiyar ruwa a tabkin Xihu. A dab da gadar Jiuquqiao, ganyayen lotus masu fadi da ke motsawa sun samar da igiya mai launin kore. Wannan ya yi kama da ganyayen lotus su mamaye duk tabkin Xihu, har ma sun hada da sararin sama. Matafiya suna sha'awar daukar hotuna kan irin wannan kyan karkara.

1 2 3