Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-28 15:41:06    
An yi addu'ar zaman lafiya a duk fadin Zimbabwe

cri

Bisa bukatar gwamnatin hadin gwiwar Zimbabwe, tun daga ran 24 zuwa ran 26 ga wata, dukkan mutanen Zimbabwe da ke zaune a gida ko kuma wadanda suke zaune a ketare ya kamata su yi addu'a, su roki gafara, ta haka za a iya fitar da jama'ar Zimbabwe daga rikicin siyasa, za a mai da hankali kan raya tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.

A watan Maris na shekarar da ta gabata, an yi babban zaben shugaban kasa a Zimbabwe tare kuma da zaben 'yan majalisar kasar da kuma na hukumomin wurare. Saboda jam'iyyun 'yan hamayya ba su gamsu da sakamakon babban zaben shugaban kasar ba, shi ya sa mabiyansu da wadanda suke goyon bayan jam'iyyar da ke mulkin Zimbabwe suka ta da rikici a tsakaninsu, wanda ya kawo wa wannan kasa baraka ta fuskar siyasa, kana kuma ya lalata tattalin arzikin kasar. A sakamakon shiga tsakani da kungiyar tarayyar raya kudancin Afirka da kungiyar tarayyar Afirka da kasashen duniya suka yi, shugabannin manyan jam'iyyu 3 na Zimbabwe sun daddale yarjejeniyar sulhuntawar harkokin siyasa daga dukkan fannoni a watan Satumba na shekarar bara, sun kuma kafa gwamnatin hadin gwiwa a watan Febrairu a shekarar bana, ta haka an sa aya ga rikicin siyasa a Zimbabwe, kuma an komar da ita kan hanyar bunkasuwa.(Tasallah)


1 2 3