Tun daga ran 24 zuwa ran 26 ga wata, an yi addu'ar zaman lafiya a duk fadin kasar Zimbabwe da zummar yakar tashin hankali. Mabambantan rukunonin siyasa da na addinai da fararen hula sun amsa kiran gwamnatin, sun yi addu'a a wurare daban daban da fatan nisantar da kasarsu daga rikicin siyasa, da maido da kwanciyar hankali da hadin kai da kuma wadata a wannan kasa.
Ran 24 ga wata da safe, shugabannin manyan jam'iyyun siyasa 3 da suka kafa gwamnatin hadin gwiwar Zimbabwe, wato shugaban Robert Mugabe da firayim minista Morgan Tsvangirai da kuma mataimakin firayim minista Mr. Mutanbala da sauran manyan jami'an gwamnatin sun ba da jagorancin yin addu'a a cibiyar taro ta kasa da kasa a birnin Harare, inda suka yi nadama kan kuskuren da suka yi a da, sun kuma yi kira ga al'ummar kasar da su nisantar da kansu daga rikicin siyasa, su kuma ba da gudummawa wajen raya Zimbabwe mai zaman lafiya da jituwa da wadata.
1 2 3
|