A yayin bikin yin addu'ar, Mr. Mugabe ya yi kira ga jam'iyyu daban daban na kasar da su sa aya ga rikicin siyasa nan da nan, su kawar da sabani cikin lumana. Ban da wannan kuma, ya bukaci shugabannin jam'iyyun su ilmantar da mabiyansu su kuma kawar da rikici cikin ruwan sanyi. Mr. Mugabe ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu an samu wasu rikice-rikicen siyasa da ba su wajaba ba a Zimbabwe. Ya kamata 'yan Zimbabwe su fitar da ruhun amincewa da mabambantan ra'ayoyi da na addini, saboda rikici ba zai iya warware kome ba.
Bugu da kari kuma, Mr. Tsvangirai ya nuna cewa, wajibi ne shugabannin jam'iyyun kasar su yi nadama kan kuskuren da suka yi a da. Yin da-na-sani zai iya taimakawa Zimbabwe wajen samun makomar zaman lafiya da jituwa. Ya kuma kara da cewa, a matsayin shugabanni, kada su take kuskurensu. Kamata ya yi su sauke nauyi domin dubban wadanda rikicin siyasa ya yi lahani gare su, ta haka za su iya tabbatar da gudanar da shirin maido da harkokin siyasa yadda ya kamata.
A cikin jawabinsa, Mr. Mutanbala ya ce, jam'iyyu 3 da ke mulkin kasar cikin hadin gwiwa kadai ba za su iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zimbabwe ba, sai dukkan jama'ar Zimbabwe sun yi kokari. Shugabannin siyasa suna iya samarwa jama'ar kasar wani dandalin tabbatar da samun kwanciyar hankali da hadin kai ne kawai.
1 2 3
|